A ranar Lahadi 13 ga wata ne aka kammala bikin bayar da lambar yabo ta Nollywood ta shekara ta 2013 (NMA 2013), lambar da aka saba baiwa taurari da masu shirya fina-finai a Najeriya.
An shirya bikin na bana ne a otel din Intercontinental, inda Rita Dominic ta lashe lambar tauraruwar fina-finai ta wannan shekara, yayin da O.C Ukeje ya lashe lambar a bangaren maza.
Ita dai Rita Dominic ta lashe lambar ce saboda rawar da ta taka a fim din nan mai suna 'The meeting', fim din da masu zabar gwarzaye 11 suka zabe shi, yayin da shi kuma Ukeje ya samu lambar bisa rawar da ya taka a fim din nan mai suna 'Phone Swap'.
Tun a shekarun 1960 ne dai sashen shirya fina-finai na Nollywood ya fara samun gindin zama a Najeriya, inda ya bunkasa cikin hanzari a shekarun 1990 da 2000, inda ya zama na biyu wajen shirya fina-finai a duniya wajen yawan fina-finan da ake samarwa a shekara, sannan yake gaban kasar Amurka, kana a bayan kasar Indiya.
Kididdiga na nuna cewa, cikin fina-finai sama da 1,500 da Nollywood din ke samarwa a ko wace shekara, kudin da yake samu ya zarce dalar miliyan 500. (Ibrahim)