Bukukuwan taron Afrika kan fina-finan shirin gaskiya (FAFD) karo na bakwai sun fara guduna tun ranar Litinin a birnin Yamai na kasar Nijar bisa taken "sabbin sinima a Afrika" a karkashin jagorancin ministan al'adun kasar Nijar, bikin FADF ya kasance wata babbar haduwa a kowace shekara, inda a tsawon kwanaki goma, masu sha'awar kallon majigi na birnin Yamai za su morewa idanunsu da kallon fina-finan shirin gaskiya kusan arba'in da manya manyan masu tsara fim na Afrika da na Turai suka shirya a cikin dakanun sinima dake birnin Yamai. Wadannan fina-finai akasarinsu na magana kan muhimman matsalolin dake haddabar kasashen Afrika a halin yanzu kamar rikicin siyasa da na jama'a a kasar RDC-Congo tare da "batun Chebaya", ko kuma "wani kisa kasa" a kasar Masar, "matan dake cikin bas mai lamba 678" da kuma wani shirin gaskiya da ya shafi rikicin kasar Cote d'Ivoire. (Maman Ada)