Cikin jawabinsa na godiya Bach, ya yabawa tsohon shugaban kwamitin Jacques Rogge, da sauran mambobin kwamitin bisa goyon baya da suka nuna masa, yana mai alkawarin yin iyakacin kokarin aiki, da sauraron ra'ayoyi daga bangarorin daban daban, don kokarta samar da daidaito da adalci ga duk wanda ya shiga wasannin Olympics, wato dai, zai zama shugaban kwamitin na kowa.
Bisa tsarin dokar shugabancin kwamitin, sabon shugaban kwamitin na da wa'adin aiki na tsawon shekaru 8 a zangon farko, da kuma karin shekaru 4, idan har ya sake lashe zabe a karo na biyu.(Bako).