Shugaba Zuma ya shaidawa mahalarta taron majalisar 'yan kasuwar kungiyar kasahen BRICS na farko a birnin Johannnesburg cewa,abu mai muhimmanci shi ne, wannan mataki zai taimaka wajen samar da yankin da za a rika gudanar da ciniki cikin 'yanci a nahiyar,tsarin da zai kai ga samar da kasuwa bai daya da kudin da ya kai dala triliyan 22.6.
Zuma ya ce wannan mataki zai taimakawa kasashen Afirka su kara bunkasa harkokin cinikayya a nahiyar,ya kuma bayyana cewa,kasashen na Afirka karkashin kungiyar AU, za su bullo da yankin ciniki cikin 'yanci,inda za su hada kan kasashen gabashi da na kudancin Afirka waje guda.(Ibrahim)