in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da kin biyan haraji
2013-08-28 10:46:19 cri

A yunkurinta na shiga a dama da ita a fagen dakile dukkanin wani yunkuri na kaucewa biyan kudaden haraji, kasar Sin ta rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwar kasa da kasa, wadanda za su taimaka wajen cimma wannan buri da aka sanya gaba.

Wang Jun, jami'i a ma'aikatar kula da harkokin tattara kudaden haraji ta kasar Sin ne ya sanya hannu kan takardun a madadin gwamnatin kasar ta Sin.

An gudanar da taron sanya hannu kan wadannan yarjejeniyoyi da babban sakataren kungiyar hadin kai ta fuskar tattalin arziki wato OECD, Angel Gurria ya jagoranta ne a jiya Talata, a helkwatar kungiyar ta OECD dake birnin Faris.

Da yake tsokaci kan wannan batu, Wang Jun, ya ce, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi kare dokokin biyan haraji. Wang Jun ya kara da cewa, hakan ya kuma zo daidai lokacin da Sin ke ci gaba da gudanar da tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki, da bude kofofinta ga kasashen ketare.

Sanya hannu kan wadannan yarjejeniyoyi da kasar Sin ta yi, ya sanya ta kasancewa kasa ta 56 da ta amince da dokokin hadin gwiwa na kasa da kasa da za mu wajabta kiyaye ka'idojin biyan haraji yadda ya dace.

Da yake yabawa wannan mataki da kasar Sin ta dauka, babban sakataren kungiyar ta OECD Angel Gurria, cewa ya yi, hakan zai dada habaka dangantakar dake tsakanin kungiyar da kuma gwamnatin kasar Sin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China