in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron karawa juna ilmi na yammacin Afrika kan haraji a Benin
2013-04-03 10:14:46 cri

Kimanin hukumomin haraji da suka fito daga kasashen yammacin Afrika goma ne suke halarta tun daga ranar Talata da ta gabata a birnin Cotonou na kasar Benin, a wani taron karama juna ilmi na shiyyar kan jigon "Tafiyar da aikin haraji, wane irin shiri ga hukumomin haraji."

Wannan zaman taron fadakarwar na tsawon mako daya, zai taimaki manyan jami'an hukumomin haraji na yammacin Afrika wajen yin nazari kan dabarun da za'a kafa domin samarwa hukumomin haraji wadatattun kudade da kayayyakin da za su samar musu damar gudanar da muhimman ayyukansu na tsare-tsaren kawo gyaran fuska da shiga cikin zamani, in ji mukadashin ministan kudi da tattalin arzikin kasar Benin, Jean Michel Abimbola.

A cewarsa, wannan jigo na da muhimmancin gaske domin ganin yadda yawan kalubalolin dake gabanmu a cikin wadannan kasashe goma dake yammacin nahiyar Afrika. Tun fiye da shekaru, kasashen goma na yammacin Afrika suka kaddamar da muhimman sauye-sauye da na zamanintarwa a cikin hukumomin haraji tare da taimakon kungiyoyin ci gaba.

Manyan jami'an hukumomin haraji dake halartar wannan dandali sun fito daga kasashen Cote-d'Ivoire, Guinia-Bissau, Mauritania, Senegal, Nijar, Burkina-Faso, Guinia, Mali, Togo da kuma Benin mai masaukin baki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China