Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ba da labari a yau ran 21 ga wata cewa, ofishin na cikin shirin hadin kai da ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen Nijeriya da Kenya, wajen shirya bikin al'adu mai taken "Fahimtar kasar Sin", da nufin zurfafa mu'ammala a wannan fanni tsakanin Sin da Nijeriya, da kuma taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Kenya.
Za a yi bikin ne daga ran 10 zuwa 29 ga watan Satumba mai zuwa a birnin Abuja, hedkwatar Nijeriya, da birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya.
Bikin "Fahimtar kasar Sin" kuwa ta zama karo na uku da kasar Sin ta shirya a nahiyar Afrika, bayan da ta taba gudanar da shi a kasashen Tanzaniya da Uganda a shekarar 2010, da kuma a kasar Jamhuriyar Kongo a shekarar 2013.
"Fahimtar kasar Sin" wani babban aiki ne ta fuskar al'adu da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya a ketare, tare da aniyar gabatar da nagartattun al'adu da fasahohin kasar Sin a kasashe daban-daban. (Amina)




