in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan a yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Koriya
2013-05-20 20:45:25 cri
A kwanan baya, kasar Koriya ta arewa ta yi ta harba makamai masu linzami masu cin gajeren zango a tekun dake gabashinta. Game da lamarin, Mr. Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau 20 ga wata, cewar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Koriya buri ne da ake son cimmawa, kuma yana dacewa da moriyar bangarori daban daban, kuma shi ne nauyi iri daya dake kansu.

Mr. Hong ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na fatan bangarori daban daban su kara daukar matakan sassauta tsananin halin da ake ciki, ta yadda za a iya kyautata huldar dake tsakanin bangarori daban daban domin kokarin cimma babban buri na tabbatar da zaman lafiya a yankin Koriya. Yana kuma fatan za a iya yin kokarin warware matsalolin dake kasancewa a gaban bangarori daban daban ta hanyar yin shawarwari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China