Kasar Sin a jiya Litinin 19 ga wata ta yi kira ga sauran kasashen duniya da su karfafa huldar dake tsakaninsu da dabaru yadda za'a cigaba wajen tunkarar matsalar 'yan fashin teku na kasar Somaliya.
Wang Min, mukaddashin wakilin din din din na kasar Sin a MDD ya bukaci hakan a wani ganawar bayyane na kwamitin tsaro na majalisar game da fashin teku.
Ya ce, "Muna fatan cewa, kasashen duniya za su cigaba da kiyaye ka'idojin MDD game da dokar teku da abin da ya jibanci hakan a kan dokokin kasa da kasa, inganta sadarwa da dabaru yadda za'a iya yakar fashin teku ta hanyar amfani da dabarun da aka tsara."
Yana mai bayanin cewa, Sin ta lura da ayyukan da suka shafi hakan, ya kamata kasashen duniya su mutunta 'yancin kasa da abin da yake mallakin kasashen da abin ya shafa.
Sin tana goyon bayan tsarin da kasashen gabar Guinea suka bullo da shi wanda suka hada da shirya wani dabaru na kasa, inganta mulkin shari'a na kasa da kasa, karfafa nagartaccen mulki da kuma kara karfin sojojin ruwa, shari'a da abubuwan tsaro domin a aiwatar da aikin da zai hana da kuma shawo kan fashin teku, in ji babban jami'in.
Mr. Wang ya yi nuni da cewa, abin da ya shafi nahiyar Afrika akwai talauci, matsalar tattalin arziki, da koma bayan ta fannin ababen more rayuwa wadanda su ne manyan dalilan da suke kawo fashin teku.
Ya ce, "Muna kira ga kasashen duniya da su inganta kokarinsu, su samar da taimako ga kasashen Afrika, musamman wadanda suke da matukar koma baya domin taka rawa wajen aiwatar da hakikanan ayyuka a wadannan kasashen ta fannin samar da dauwamammen cigaba, yaye talauci da kuma samar da tattalin arziki da abababen more rayuwa."(Fatimah)