in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Aljeriya ya nada sabon firayin ministan kasar
2012-09-04 09:42:24 cri

A Jiya 3 ga wannan wata, shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya nada Abdelmalek Sellal wanda shi ne mutum mai zaman kansa a matsayin firayin ministan sabuwar gwamnatin kasar don maye gurbin firayin ministan tsohuwar gwamnati Ahmed Ouyahia.

An kafa sabuwar majalisar dokokin jama'ar kasar Aljeriya ne a ranar 10 ga watan Mayun shekarar bana ta hanyar jefa kuri'a, amma ba a kafa sabuwar gwamnatin kasar ba tukuna. Bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar, firayin ministan kasar ne ya kamata ya gabatar da sunayen mambobin gwamnatin kasar tare da samun amincewar shugaban kasar.

An haifi Sellal ne a ranar 1 ga watan Agustan shekarar 1948 a birnin Constantine dake arewa maso gabashin kasar Aljeriya, ya gama karatu a kwalejin koyar da ilmin tafiyar da harkokin kasa ta kasar, daga baya, ya kuma rike wasu mukamai kamar su ministan kula da harkoki cikin gida da kananan gwamnatocin birane na gwamnatin kasar Aljeriya, ministan kula da harkokin matasa da wasannin motsa jiki, ministan kula da gine-ginen gwamnati, ministan sufuri da sauransu. Kana ya taka muhimmiyar rawa yayin da shugaba Bouteflika ya shiga babban zaben shugaban kasar sau biyu wato na shekarar 2004 da ta 2009. Kafin a nada shi a matsayin firayin ministan kasar, shi ne ministan kula da albarkatan ruwa na kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China