Shugaban asusun ba da lamuni na duniya IMF Christine Lagarde a jiya Lahadi ta sanar da cewa, asusun zai bude wata sabuwar cibiyar horaswa na shiyya a Afrika.
Lagarde ta sanar da hakan ne bayan wata ganawa da ta yi da jigogin asusun na nahiyar Afrika, inda a sanarwar da ta fitar, ta ce, asusun zai bude cibiya ta 6 domin ba da horon sanin makaman aiki a Accra, babban birnin kasar Ghana wanda zai taimaka gaya ma kasashen da ba su amfani da harshen Faransanci a nahiyar.
Ta kuma sanar da cewa, cibiyar koyar da sanin makaman aiki da aka bude a kasar Mauritaniya a watan Disamban shekara ta 2012 zai fara aiki a nan da 'yan watanni masu zuwa, inda zai hadu da sauran cibiyoyin a sauran sassan duniya domin taimaka ma kasashe masu tasowa su samu sanin makaman aiki a fannin shugabanci zuwa bangaren tattalin arziki da aiki da shi sosai.
Sanarwa ta kuma lura da cewa, yawancin kasashe a hamadar Sahara na Afrika na cigaba da samun karuwar al'umma, sai dai kuma ababen samun kudi a matsakaitan kasashen a nahiyar na tafiyar hawainiya, abin da ke da nasaba da yanayin kasuwanci da kasashen Turai, da wassu kasashe a arewacin nahiyar Afrika, da kuma sarkakkiyar yanayin sauyin siyasa.(Fatimah)