Wata sanarwa da asusun wanda ke da zama a Washington ya bayar, ya bayyana cewa, wannan wani bangare na goyon bayan hukumomin Mali da shawarwari da kuma taimakon kudi ta yadda za su daidaita tare da bunkasa tattalin arzikin kasar cikin watanni 12 masu zuwa, bisa taimakon da abokan huldar Mali ke bayarwa.
Mataimakin manajan darektan asusun na IMF Zhu Min ya ce, "an tsara shirin rancen ne don taimakawa Mali ta gaggauta biyan ragowar kudin da ake bukata wadda zai share mata hanyar samun tallafin kudi daga abokan huldarta na kasa da kasa, wanda wannan wata babbar matsala ce ga farfadowar tattalin arzikin kasar ta Mali. (Ibrahim)