Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kulla yarjeniyoyi da dama a bangren samar da ingantattun na'urori a bikin CIIE
2020-11-09 10:29:26        cri
Wani rukunin kamfanoni mallakar gwamnati daga Shanghai, ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi 16 a karshen mako, yayin da ake ci gaba da gudanar da baje kolin kayayyakin da ake shigo da su Sin wato CIIE.

Daraktan cibiyar kula da kadarorin gwamnati ta Shanghai, Bai Tingui, ya ce kamfanonin mallakar gwamnati, za su yi amfani da bikin CIIE a matsayin wata dama ta fadada hadin gwiwarsu da musaya da bude kofa da kuma taka rawa wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Galibin masu zuba jari sun fi mayar da hankali kan ingantattun na'urorin zamani, yayin da masu kera na'urori ke kara shiga ayyuka a kasar Sin.

Har ila yau yayin bikin, kamfanonin lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, daya daga cikin larduna mafi hada-hadar tattalin arziki a kasar, su ma sun cimma yarjeniyoyin hadin gwiwa, tare da rattaba hannu kan kwangiloli.

Kididdiga daga sashen kula da cinikayya na lardin ta nuna cewa fitattun kamfanoni 28 a lardin da masu baje koli 28 daga kasashe sama da 10, ciki har da Jamus da Japan da Amurka, sun rattaba hannu kan wasu shirye-shirye 31, da suka kunshi na'urorin da ake amfani da su a masana'antu da bangaren kiwon lafiya, inda jimilar darajar kwangilar ta kai yuan biliyan 12.79, kwatankwacin kimanin dala biliyan 2. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China