Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin Afirka ta kudu: CIIE zai taimakawa 'yan kasuwa farfadowa bayan COVID-19
2020-11-06 15:43:50        cri

Babban jami'i a rukunin bankin Standard Bank na kasar Afirka ta Kudu Philip Myburgh, ya bayyana cewa, bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin(CIIE) zai baiwa 'yan kasuwa da kamfanonin kasar Sin damar tattaunawa da ma kulla yarjeniyoyi, matakin da zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Afirka bayan annobar COVID-19.

Jami'in rukunin bankin shi ma ya halarci bikin baje kolin na CIIE na wannan shekara, ya bayyana cewa, bikin ya zo a lokacin da harkokin cinikayya ke cikin wani yanayi mai sarkakiya, saboda halin da tattalin arzikin ya tsinci kansa sakamakon COVID-19.

Ya ce, yana da muhimmanci, "mu zakulo sabbin hanyoyi na hade kwastomominmu da kasuwannin dake da damammaki ga 'yan kasuwar Afirka, ta yadda za su fadada harkokinsu har ma su bunkasa. Yana kuma fatan cewa, 'yan kasuwar Sin da Afirka, za su kara yin cudanya a nan gaba, wadda za ta haifar da kyawawan sakamako ga nahiyar baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China