Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nuna kayayyakin kasashe masu alaka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" a bikin CIIE
2020-11-08 16:35:06        cri

 

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin (CIIE) karo na 3, a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. Inda a cikin wani dakin musamman da aka kebewa kayayyaki na wasu kasashe masu alaka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", an nuna sabbin kayayyaki masu inganci iri-iri, don jama'a su gwada kayayyakin da kuma sayensu, ta yadda suke samun damar kara sanin kasashe da yakuna dake dab da "Ziri Daya da Hanya Daya".

Hakika an kaddamar da wurin nuna kayayyakin kasashe daban daban kafin a fara aiwatar da bikin CIIE karo na 2. Kana a wannan karo, an nuna kayayyakin da aka samu daga rumfunan kasashe da yankuna fiye da 20, wadanda suka hada da Thailand, da Sifaniya, da Japan, da Koriya ta Kudu, da Rasha, da Syria, da Iran, da Afirka ta Kudu, da dai sauransu.

An ce, an samu kafa wannan wurin nuna kayayyakin kasashe daban daban ne, bisa tushen cibiyar nuna kayayyakin mabambantan kasashe ta yankin ciniki mai 'yanci na birnin Shanghai. Bayan da aka kaddamar da cibiyar a shekarar 2014, ta riga ta zama wani muhimmin dandali, inda kasar Sin da sauran kasahse da yankuna za su iya mu'amala da hadin gwiwa da juna a fannonin kayayyaki, da tattalin arziki, gami da al'adu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China