Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Morocco: Jawabin Xi Jinping na bude bikin CIIE ya samar da sako mai yakini a duniya
2020-11-08 16:18:35        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a yayin taron bude bikin baje kolin kayayyaki da ake shigowa da su kasar Sin daga waje karo na 3 wato CIIE, abun da ya jawo hankalin masanan ketare matuka. Shugaban kungiyar hadin kai da samun bunkasuwar Afrika da Sin na kasar Morocco Nasser Bouchiba ya shedawa manema labarai na CMG cewa, jawabin shugaba Xi ya bayyana niyyar Sin na kara bude kofarta ga ketare, matakin ba kawai ya samarwa duniya damammaki masu kyau ba ne, har ma ya goyi bayan kasashe masu tasowa.

Nasser Bouchiba masana ne a fannin hadin kan Sin da Afrika, ya kafa wannan kungiya ne a shekarar 2018, don dukufa kan ba da taimako kan hadin kan Afrika da Sin a fannoni daban-daban. Yana mai cewa, Sin ta more kasuwsanninta da kasashen duniya ba tare da boye-boye ba, matakin da ya ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya, ita ma ta bayyana matsayinta na wata babbar kasa dake sauke nauyin dake bisa wuyanta, ban da wannan kuma, matakan da take dauka na karawa jama'ar duniya kwarin gwiwa duba da illar da cutar COVID-19 take kawowa duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China