Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WTO ta dage yanke shawara game da sabon shugabanta
2020-11-07 17:17:54        cri

Hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta sanar da dage babban taronta na musammam kan nadin sabon darakta janar na hukumar da aka shirya yi a ranar 9 ga wata, bisa dalilan da suka hada da lafiya da kuma yanayin da ake ciki a yanzu.

Shugaban majalisar hukumar David Walker na kasar New Zealand, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya aikewa dukkan mambobin hukumar cewa, an sanar da shi cewa, bisa dalilai na lafiya da abubuwan dake faruwa yanzu, wakilai ba za su iya yanke shawara a hukumance ba a ranar 9 ga wata kamar yadda aka tsara. A don haka, ya dage taron zuwa wani lokaci, yayin da zai ci gaba da tuntubar wakilan.

A ranar 28 ga watan Oktoba ne David Walker, ya shaidawa mambobin WTO yayin wani taro cewa, bisa la'akari da tuntubar dukkanin wakilai, Ngozi Okonjo-Iweala, yar asalin Nijeriya ce 'yar takarar mafi dacewa, wadda kuma aka cimma matsayar cewa za ta zama sabuwar darakta janar ta hukumar.

Sai dai kuma, Amurka ta kalubanci wannan matsaya, inda ta ce za ta ci gaba da mara baya ga ministar cinikayya ta Koriya ta arewa wato Yoo Myung-hee, kuma ba za ta goyi bayan takarar Ngozi Okonjo Iweala ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China