Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta lashi takwabin ganin Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar WTO
2020-10-30 20:02:25        cri
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, ta lashi takwabin tabbatar da cewa, 'yar takarar ta dake namen kujarar shugabancin kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) Dr. Ngozi Okonja-Iweala ta zama shugabar kungiyar, duk da tsaikon dake gabanta.

Wata sanarwa da kungiyar WTO ta fitar a hukumance ranar Larabar da ta gabata, ta bayyana cewa, an gabatar da tsohuwar ministar kudin kasar ta Najeriya, don zama sabuwar babbar darektar kungiyar mai hedkwata a birnin Geneva, yayin wani taro da aka gudanar a asirce, inda aka tantance cewa, 'yar takarar tana da kyakkyawar damar samun amincewar mambobin kungiyar.

Mai magana da yawun WTO Keith Rockwell ya bayyana cewa, kasar Amurka ce kadai take kin mara mata baya, wadda ta ce za su ci gaba da goyon bayan, ministar kasar Koriya ta kudu Yoo Myung-hee.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, yana da muhimmanci a fahimci cewa, Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan bangarorin shiyyoyi da dama, in ban da Amurka.

A ranar 9 ga watan Nuwanba ne, za a gabatar da takarar Dr.Okonjo-Iweala, yayin babban taron kungiyar, idan aka amince da ita, za ta kasance mace ta farko kuma 'yar Afirka da za ta shugabanci kungiyar cikin tarihin shekaru 25 da kafuwarta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China