2019-05-21 10:20:11 cri |
Wasu alkaluma da kungiyar cinikayya ta duniya ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa, bunkasur cinikayyar duniya za ta ci gaba da raguwa har zuwa rubu'i na biyu na shekarar 2019 da muke ciki.
Hasashen baya-bayan da kungiyar ta fitar na kaso 96.3, ya yi kasa da maki 100 na alkaluman, wanda ya kasance mafi koma baya tun a shekarar 2010, alamun da ke nuna ci gaban raguwar bunkasar cinikayya a watanni shida na farko na shekarar 2019.
Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa, yanayin harkokin cinikayya na iya kara kazanta, idan har ba a warware takaddamar cinikayya ko kuma sashen dake nazartar yanayi da karfin tattalin arziki suka gaza dacewa da yanayin da ake ciki.
Bugu da kari, duk wani canji da za a samu a shekarar 2020, ya dogara ne kan rage tankiyar cinikayya ko inganta sashen dake nazartar tsari da yanayin tattalin arziki .(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China