Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan takara mata biyu sun kai zagayen karshe a neman shugabancin WTO
2020-10-08 21:20:35        cri
Mata 'yan takara biyu, Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya, da Yoo Myung-hee, daga Koriya ta kudu, sun kai zagayen karshe na takarar neman shugabancin kungiyar ciniki ta duniya WTO.

Sakamakon ya kafa wani muhimmin tarihi tun kafuwar kungiyar ta WTO a shekaru 25 da suka wuce, hakan ya bada tabbaci karo na farko ne da mace za ta zama darakta janar ta kungiyar WTO inda zata ja ragamar shugabancin kungiyar, a cewar sanarwar da kungiyar ta fitar.

Kakakin kungiyar ya bayyana cewa, za a gudanar da zagaye na uku kuma na karshe na tuntuba a tsakanin mambobin WTO daga 19 zuwa 27 ga watan Oktoba, inda ake sa ran za a daddale wacce zata dare shugabancin kungiyar ta WTO a karo na gaba.

An fara shirye shiryen zabar sabon shugaban ne tun a ranar 14 ga watan Mayu, bayan da darakta janar na hukumar Roberto Azevedo ya sanar da mambobin WTO cewa zai yi murabus shekara guda gabanin cikar wa'adin aikinsa a yayin da yake wa'adi na biyu na shugabancin kungiyar. Tun a ranar 31 ga watan Ogasta ya sauka daga mukaminsa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China