Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su yi amfani da albarkatun dake akwai wajen shawo kan tasirin COVID-19 a kan tattalin arziki
2020-11-07 17:12:55        cri

Kungiyar Tax Justice Network Africa (TJNA), mai nazarin harkokin kudi da haraji a Afrika, ta bukaci kasashen nahiyar su yi amfani da kudaden shigar da ake samu daga albarkatun karkashin kasa domin tunkarar matsalar tattalin arziki dake alaka da annobar COVID-19.

Babban daraktan kungiyar, Alvin Mosioma, ya ce za a iya amfani da kudin da ake samu daga bangaren albarkatun karkashin kasa wajen cike gibin kasafin kudi a nahiyar yayin da ake fama da COVID-19.

Ya ce raguwar ci gaban tattalin arziki saboda annobar na iya tarnaki ga samar da muhimman hidimomi a Afrika, wadanda suka shafi bangarorin lafiya da na ilimi da tsaftataccen ruwan sha, yana mai cewa, albarkatun karkashin kasa da nahiyar ke da su na da damar samar da mafita.

Kiddidigar bankin raya nahiyar AFDB, ta nuna cewa, talauci ya karu a nahiyar saboda kalubalen da annobar ta haifar.

Bankin ya ce COVID-19 ka iya jefa karin mutane miliyan 28.2 zuwa miliyan 49.2 na nahiyar cikin matsanancin talauci, wanda kuma zai kawo cikas ga kokarinsu na ba da gudunmuwa ga ajandar sauyi ta nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China