Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: FOCAC ya samar da damammakin ci gaban Afirka
2020-11-06 19:08:58        cri

A yau Alhamis ne aka bude taro na 9, na masanan Sin da Afirka game da dandalin hadin gwiwar sassan biyu na FOCAC, ta yanar gizo da kuma gaba da gaba.

Yayin taron mai taken "Cikar FOCAC shekaru 20: waiwaye da lura da inda aka dosa ", wani masani a cibiyar nazarin harkokin Afirka dake jami'ar horas da malamai ta Zhejiang ta nan kasar Sin, kuma 'dan asalin tarayyar Najeriya Osidipe Adekunle, wanda ya halarci taron ta yanar gizo, ya ce dandalin FOCAC ya samar da wata dama, ta hade al'ummun Sin da na nahiyar Afirka, tare da bude damammakin wanzar da ci gaba na kai tsaye ga nahiyar Afirka.

Osidipe Adekunle, ya jaddada cewa, akwai manyan damammaki na raya hadin gwiwar Sin da Afirka karkashin tanadin manufofin FOCAC. Ya ce ya dace masanan Sin da na Afirka su karfafa musayar bayanai, da tsara harkokin hadin gwiwa, da ma musaya tsakanin al'ummun su da fannin raya al'adu. Kaza lika su yi aiki tare, wajen samar da murya guda a mataki na kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China