Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta yi aiki da 'yan uwanta na Afirka wajen gina al'umma guda mai makomar bai daya
2020-11-06 19:23:05        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce duk irin hadurra da kalubale da za a iya fuskanta, Sin za ta yi tarayya da 'yan uwanta na Afirka, wajen ingiza kafuwar al'umma guda mai makomar bai daya, za ta kuma ci gaba da daga tutar abuta ta Sin da nahiyar Afirka. Wang Wenbin ya bayyana hakan ne a yau Juma'a, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, dukkanin kayayyakin kiwon lafiya da gwamnatin Sin ta baiwa kasashen Afirka 53 don yaki da cutar COVID-19, domin amfanin mata da yara kanana da ma manya, sun isa kasashen ta hannun kungiyar samar da ci gaba ta matan shugabannin nahiyar.

Da yake karin haske game da hakan, Wang Wenbin ya ce, duk da kalubalen dakatar da sufuri tsakanin kasa da kasa, Sin ta cimma nasarar mika wadannan kayayyaki zuwa kasashen cikin watanni 4. Kuma gwamnatocin kasashen nahiyar da al'ummun su, sun jinjinawa wannan kwazo, suna masu bayyana tallafin a matsayin wani mataki, da ya karfafa ikon matan Afirka, da yara da ma manya na shawo kan cutar COVID-19.

Kaza lika sun bayyana hadin gwiwar sassan biyu, da goyon bayan juna, da hadin kan su, a matsayin muhimmin jigo na yakar annobar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China