Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da bikin matasan Sin da Afrika na cikar FOCAC shekaru 20
2020-10-27 10:29:38        cri

An kaddamar da bikin matasan Sin da Afrika karo na 5 jiya Litinin a nan birnin Beijing, domin murnar cikar dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika shekaru 20 da kafuwa.

Yayin bikin na kwanaki 7, wakilan matasan Afrika 42, za su ziyarci masana'antu da cibiyoyin fasahohin zamani dake Beijing da lardin Jiangxi na gabashin kasar Sin, kana za su tattauna da wakilan matasan kasar Sin.

Da yake jawabin bude bikin, Wang Jiarui, shugaban gidauniyar China Soong Ching Ling, daya daga cikin mashirya bikin, ya ce tun bayan kaddamar da shi karon farko a shekarar 2016, bikin ya zama wani dandali mai muhimmanci ga matasan Sin da kasashen Afrika, wajen zurfafa mu'amala da fahimtar juna.

Shi kuwa mataimakin ministan harkokin wajen Sin, Deng Li, ya karfafawa matasan bangarorin biyu gwiwar aiki tare cikin hadin kai domin inganta dandalin FOCAC. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China