Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwar Sin da Afirka na ci gaba da bunkasa
2020-10-12 20:51:42        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai Litinin din nan cewa, har yanzu ba a kammala bunkasa alakar dake tsakanin Sin da Afirka ba. Yana mai cewa, sassan biyu za su yi amfani da bikin cika shekaru 20 na kafuwar dandalin FOCAC, a matsayin wata dama, ta gina makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka, wadda za ta amfanin al'ummomin sassan biyu.

Ya ce, a cikin shekaru 20 da suka gabata, dandalin ya kasance mai muhimmanci, kana wata kafa ta yin shawarwari, muhimmiyar kafar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kana wata muhimmiyar alakar hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Kasashen Sin da Afirka za su ci gaba da tuntubar juna, da yin musaya da inganta matakan raya dandalin da bunkasa aiwatar da nasarorin da aka cimma, da ciyar da hadin gwiwar sassan biyu bisa manyan tsare-tsare gaba, da mayar da hadin gwiwar Sin da Afirka a matsayin abin koyi na cudanyar bangarori daban-daban, da cin moriyar juna da samun nasara tare, da ci gaba da bayar da gudummawa wajen kare daidaito da adalci a harkokin kasa da kasa, da yayata bukatar bunkasuwa da makomar duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China