Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana dora muhimmanci kan soke bashin da ake bin Afirka
2020-10-12 20:46:15        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasarsa tana dora muhimmanci game da batun soke bashin da ake bin kasashen Afirka. Haka kuma tana son ganin an aiwatar da shirin soke bashin da ake bin kasashen nahiyar da kungiyar G20 ta gabatar.

Zhao Lijian wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, ya bayyana cewa, a baya-bayan nan wasu kafofin watsa labarai sun watsa rahotanni dake cewa, wasu kasashen yamma, sun zargi kasar Sin da "daba tarko bashi" a Afirka, ta hanyar kin shiga shirin G20 na ragewa kasashen na Afirka bashin da ake binsu, da kuma gazawa wajen taimakawa kasashen na Afirka rage musu tarin bashin da ake bin su.

Kan wannan batu, Zhao Lijian, ya yi nuni da cewa, har kullum hadin gwiwar Sin da Afirka tana nan daram, ta rashin tsoma baki a harkokin cikin gidansu, ba kuma tare da gindaya wani sharadi na siyasa ba. Kuma wannan ita ce manufar da Sin take bi kan batun da ya shafi bashin da ake bin kasashen na Afirka, don haka, kasar Sin ba ta danawa Afirka tarkon bashi ba.

Ya ce, a matsayinsa na bankin da ya ke bayar da rance a hukumance, bankin shigi da fice na kasar Sin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar sokewa kasashen Afirka 11 bashi. Haka kuma kasar Sin, za ta soke rance marasa kudin ruwa da ya kamata wasu kasashen Afirka 15 su biya a karshen 2020, za kuma ta ci gaba da ingiza kasashen duniya, musamman G20, da su kara wa'adin biyan bashin da ake bin kasashen.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China