Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai bukatar ingiza dangantakar Sin da Amurka bisa turbar da ta dace
2020-11-05 14:56:30        cri
A yau Laraba, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira wani taron manema labarai, kan taron majalisar shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO, wanda Shugaba Xi Jinping zai halarta.

Yayin taron kuma, mataimakin ministan harkokin wajen Sin Le Yucheng, ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan zaben shugaban kasar Amurka da kuma tasirinsa kan dangantakar Sin da Amurka.

A cewarsa, har yanzu ba a kai ga fitar da sakamakon zaben ba, yana mai fatan za a kammala ba tare da wata tangarda ba. Ya ce kyautata dangantakar Sin da Amurka ba muradi ne na kasashen biyu da al'ummominsu kadai ba, har ma da daukacin al'ummar duniya.

Ya kara da cewa, yana fatan sabuwar gwamnatin Amurka za ta hada hannu da Sin, wajen daukaka dangantakarsu ta hanyar zaman lafiya ba tare da fito na fito ba, bisa mutuntawa da moriyar juna da kuma mayar da hankali kan hadin gwiwa da hukuri da juna da ingiza dangantakar bisa turba madaidaiciya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China