Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin: dan siyasan Amurka yana kallon kasar Sin bisa tunaninsa kawai
2020-10-22 21:21:48        cri

Kwanan baya, mai ba da shawara ga shugaban kasar Amurka dangane da harkokin tsaron kasa Robert C. O'Brien, ya yi wasu kalamai na bata matsayin tunanin JKS.

Dangane da kalaman nasa ne kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana yau Alhamis a nan Beijing cewa, O'Brien ya yi wannan bayani ne saboda yana kallon kasar Sin bisa tunaninsa kawai, kuma yana rungumar tunanin yakin cacar baka.

Zhao ya ce kalaman O'Brien ba su yi tafiya daidai da zamani ba. Babu kuma wanda zai amince da shi. Kuma tabbas ba zai yi nasara ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China