Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kakabawa wasu kamfanonin Amurka da daidaikun mutane takunkumi kan shirin sayarwa yankin Taiwan makamai
2020-10-26 20:48:29        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sanar a Litinin din nan cewa, kasarsa ta yanke shawarar kakabawa wasu kamfanonin Amurka dake da hannu a shirin Amurkar na sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makamai, da kuma wasu daidaikun mutane da hukumomi da suka taka muhimmiyar rawa a wannan batu, a matsayin wani muhimmin mataki na kare muradunta.

Zhao Lijian ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa kan wannan batu. Kamfanonin kasar ta Amurka dake da hannu damu-damu a wannan lamari, sun hada da Lockheed Martin, da Boeing Defense da kuma Raytheon.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China