Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kashe triliyoyi a fannin ilmi a shekarar 2019
2020-11-05 12:24:42        cri

Yawan kudaden da kasar Sin ta zuba a fannin ilmin kasar a shekarar 2019 ya zarce kudin kasar Yuan triliyan 5 kwatankwacin dala biliyan 748.8, a karon farko, an samu karin kashi 8.74 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarun da suka gabata wanda ya kai Yuan triliyan 4.6, kamar yadda alkaluman da ma'aikatar ilmin kasar ta bayyana.

Kudaden da gwamnatin Sin take kashewa a fannin ilmi ya zarce Yuan triliyan 4, wato ana samun karin kashi 8.25 bisa idan an kwatana da makamancin shekarar da ta gabata, a cewar ma'aikatar ilmin, adadin ya kai kashi 4.04 na karfin tattalin arzkin GDPn kasar.

Alkaluman sun nuna cewa, adadin kudaden yau da kullum da ake kashewa a fannin ilmin kasar ya zarce kashi 4 bisa 100 na yawan GDPn kasar na shekaru takwas a jere tun daga shekarar 2012. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China