Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sana'o'in da suka lambobin yabo a kasar Sin sun samu riba mai yawa
2020-11-03 11:01:54        cri
Hukumar kare 'yancin mallakar fasaha ta kasar Sin (NIPA) ta bayyana cewa, tamburan sana'o'in da suka lashe lambonbin yabo na kasar, sun samu gagarumar riba, matakin da ya kara karfafa inganta 'yancin mallakar fasaha na kasar

Da yake karin haske yayin taron manema labarai da hukumar ta shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, jami'in hukumar Lei Xiaoyun ya bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2018, ayyukan da suka shafi sana'o'i 40 dake sahun gaba da suka lashe lambar yabon hukumar karo na 21, sun samu ribar sayar da kayayyaki ta Yuan biliyan 660, kimanin dala biliyan 98.7 da ribar da ta kai Yuan biliyan 62.9, sai kuma ribar fitar da kayayyaki da ta kai Yuan biliyan 136.3.

A cewar Lei, tamburan sana'o'i 2,479 ne suka shiga gasar ta wannan shekarar, kuma daga cikinsu, kaso 62 cikin 100 na sana'o'i masu fasahar kirkire-kirkire 766 da suka lashe lambar suna cikin rukunin sabbin masana'antu ne, kana kaso 83 cikin 100 suna cikin rukunin manyan masana'antu. Ya kara da cewa, galibin ayyukan da suka lashe lambobin yabon, sun kunshi masana'antu da muhimman fasahohi na kere-kere. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China