Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karin kasashen 8 sun kaddamar da cibiyar Confucius ko azuzuwan koyon Sinanci a bana
2019-12-12 10:37:05        cri
Rahotanni daga taron kasa da kasa game da koyar da yaren Sinanci na bana, wanda ya gudana a lardin Hunan na nan kasar Sin sun nuna cewa, a shekarar nan ta 2019, an samu karin kasashe 8 da ko dai suka kafa cibiyar koyar da harshe da al'adun Sin ta Confucius, ko kuma azuzuwan koyar da Sinanci.

Taron wanda aka kammala a ranar Talata, ya nuna cewa, kasashen da suka shiga jerin a bana sun hada da Haiti, da janhuriyar Afirka ta tsakiya, da Chadi da Korea ta kudu, da Dominica, da Timor-Leste, da tsibirin Maldives da kuma kasar Saudiyya.

Da wannan sakamako, yawan kasashe da yankunan dake da cibiyoyin koyon Sinanci sun kai 162, wadanda suka kafa cibiyoyin Confucius 550, da kuma azuzuwa 1,172. A shekarar ta bana kadai, an samar da karin cibiyoyin Confucius 27, da kuma sabbin azuzuwan koyon Sinanci 66.

Da yake tsokaci yayin rufe taron na bana, mataimakin minista a ma'aikatar ilimin kasar Sin Tian Xuejun, ya ce wadannan cibiyoyi da azuzuwa, na zama wata gada dake ba da damar zurfafa fahimtar juna, da inganta sadarwa, da fadada hadin gwiwa tsakanin sassan duniya daban daban. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China