![]() |
|
2020-11-05 12:21:27 cri |
Li ya yi wannan tsokaci ne a lokacin ziyarar duba ayyuka a lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin tsakanin ranakun Talata zuwa Laraba.
Ya ce kamata ya yi a dauki matakan inganta tsarin aiwatar da sabbin manufofin cigaba da kuma tsara sabbin matakan bunkasa ci gaban kasar, gami da samar da ci gaba mai inganci.
A lokacin da ya ziyarci yankin da ake noma alkamar hunturu a kauyen Donglu na birnin Anyang, Li ya duba yanayin kasar noman kana ya tattauna da manoman yankin da kuma kwararrun masana ayyukan gona.
Li ya jaddada muhimmancin inganta samar da nau'ikan kayan amfanin gona iri daban daban, da amfanin gona masu inganci domin samun karuwar yabanya, kana ya karfafawa hukumomin ayyukan gona na yankin gwiwa da su rungumi tsarin aikin gona na zamani, kuma su aiwatar da manufofin inganta aikin gona idan damar hakan ta samu. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China