Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: Akwai muhimmancin tsara shirin da ya dace domin raya kasar Sin tsakanin 2021-2025
2020-11-01 16:22:31        cri

A ranar 30 ga watan Oktoban da ya gabata, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya kira taron tawagar jagorancin aikin tsara daftarin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 14 na kasar Sin na majalisar gudanarwar kasar, inda ya yi nuni da cewa, har yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, a don haka ya dace a tsara shirin raya kasa bisa hakikanin yanayin da take ciki, haka kuma ya dace a kara maida hankali kan ci gaban kasar, ta hanyar kara karfafa kirkire-kirkire, da kafa tsarin masana'antun zamani, da kara habaka bukatun cikin gida, da sa kaimi kan cudanya a kasuwanni cikin gida da na ketare, da kara karfafa gina wayewar kai a bangarorin halittu masu rai da marasa rai, da daga matsayin rayuwar al'ummun kasar da sauransu, kana ya dace a kara ba da muhimmanci kan wasu manyan ayyukan dake shafar rayuwar al'ummun kasar, musamman wajen ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kula da tsoffi da kuma yara kanana.

Li Keqiang ya kara da cewa, yayin da ake tsara shirin raya kasar, kamata ya yi a maida hankali kan amfanin kasuwa da amfanin gwamnati, tare kuma da zurfafa kwaskwarima kan wasu muhimman fannoni, ta yadda za a samar da muhallin kasuwanci mai inganci bisa doka, tare kuma da kara kuzarin ci gaban kasuwa a kasar, ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga ketare ta hanyar daukar matakai masu karfi da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, a karshe dai za a cimma burin samun moriya tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China