Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya jaddada muhimmancin kara kuzarin tattalin arzikin duniya
2020-09-17 20:51:27        cri

Yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi tsokaci game da taron tattaunawar 'yan kasuwan kasa da kasa na musamman yayin taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da firayin ministan kasar Li Keqiang ya halarta, inda ya bayyana cewa, yayin taron, firayin minista Li ya gabatar da wani jawabi, inda ya jaddada cewa, ya dace bangarori daban daban su sauke nauyin dake bisa wuyansu, haka kuma su goyi bayan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, tare kuma da kiyaye tsarin kasa da kasa, saboda hakan zai kawo fata da imani ga al'ummun kasashen duniya, kana ya kara da cewa, idan ana son saukaka cinikayya da zuba jari a fadin duniya, kamata ya yi a gaggauta maido da tsarin samar da kayayyakin kasa da kasa, ta yadda za a kara kuzarin tattalin arzikin duniya.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da manema labaran da aka kira yau, yana mai cewa, firayin minista Li ya furta cewa, kasar Sin za ta cimma muradun da aka tsara a fannin ci gaban tattalin arzikin kasar, ya kuma jaddada cewa, tattalin arzikin kasar Sin a hade yake da tattalin arzikin duniya, duk da cewa, an yi manyan sauye-sauye a halin da ake ciki yanzu, amma kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar zurfafa kwaskwarima da habaka bude kofa ga ketare. Ban da haka kasar Sin za ta kara karfafa cudanyar jama'a tsakanin kasa da kasa yayin da ta yi nasarar kawo karshen yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, domin samar da yanayin kasuwanci mai inganci ga manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda ke gudanar da harkoki tsakanin kasa da kasa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China