Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin kasashen duniya: Bikin CIIE na kasar Sin na gabatar da damarmaki da bunkasa farfadowar duniya
2020-11-05 10:40:34        cri
Shugabannin kasashen duniya, sun bayyana bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su Sin karo na 3 wato CIIE, a matsayin wanda zai samar da sabuwar dama ga ci gaban duniya da kuma karfafa tsarin cinikayya da tattalin arzikin duniya dake cikin wani yanayi.

Da suke jawabi ta kafar bidiyo yayin bude bikin, shugabannin kasashe da dama sun yabawa nasarar kasar Sin ta fuskar shawo kan kalubalen da COVID-19 ta haifar da kuma gudanar da bikin CIIE karo na 3, kamar yadda aka tsara.

Da yake jawabi, shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya godewa shugaba Xi Jinping da al'ummar Sinawa, bisa magance matsalolin da suka taso da kuma gudanar da bikin kamar yadda aka tsara, yana mai cewa, inganta cinikayya da zuba jari na da matukar muhimmanci ga farfadowar tattalin arziki daga halin da yake ciki a yanzu.

Da yake bayyana cewa nahiyar Afrika na kokarin kafa yankin ciniki cikin 'yanci, shugaba Ramaphosa ya ce kasar Sin daddadiyar abokiyar cinikayya ce, kuma bikin CIIE ya samar da wani muhimmin dandali ga kasashe da kamfanonin Afrika. Ya ce Afrika ta kudu ta halarci bukuwan CIIE na baya, yana mai yi wa bikin na wannan karo fatan nasara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China