Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Ya dace a ingiza gina tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba ta hanyar tattaunawa
2020-11-04 21:03:22        cri

Yayin bikin kaddamar da bikin CIIE karo na uku, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya dace a nace kan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa ta hanyar tattaunawa, tare kuma da kiyaye tsarin cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban karkashin jagorancin hukumar cinikayyar duniya, ta yadda za a ingiza gina tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba.

Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta gabatar da manufar kara cudanya a kasuwar gida, tare kuma da kara cudanya a kasuwannin kasa da kasa, domin biya bukatun gida, tare kuma da amfanin al'ummun kasa da kasa.

Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana da al'ummu masu yawan biliyan 1.4, a ciki, adadin mutanen da suka samu kudin shiga har kudin Sin yuan wajen dubu biyar a kowanne wata ya kai miliyan 400, a don haka kasar Sin ta kasance babbar kasuwa a duniya, har ma ana hasashen cewa, a cikin shekaru goma masu zuwa, gaba daya adadin kayayyakin da za a shigo da su kasar Sin zai kai dala triliyan 22.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China