Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Tattalin arzikin Sin ya nuna alamun bunkasa cikin rubu'i 3 na farkon shekarar bana
2020-11-04 21:14:42        cri
A gun bikin bude bikin baje kolin CIIE karo na 3, Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, bayan da jama'ar kasar Sin suka yi kokari tare, an samu nasarori kan yaki da cutar COVID-19. Tattalin arzikin Sin ya nuna alamun bunkasa cikin rubu'i 3 na farkon shekarar bana, yayin da cinikayyar waje ta karu da kaso 0.7 bisa dari, kana yawan jarin waje da aka yi amfani da shi ya karu da kaso 5.2 bisa dari.

Xi ya jadadda cewa, Sin za ta ci gaba da martaba manufofin bude kofa ga kasashen waje da hadin gwiwa don moriyar juna, wajen kara bude kofa ga kasashen waje daga dukkan fannoni. Kana za ta kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasuwar cikin gida da na waje, da more albarkatun juna, a kokarin mayar da kasuwar Sin kasuwar duniya, wadda kowa zai amfane ta, kuma kowa zai iya shigar ta. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China