2020-10-16 11:20:41 cri |
A yanzu haka, kasa da makonni uku ne suka rage za a bude bikin baje kolin na CIIE karo na uku. Kakakin ma'aikatar Gao Feng ya bayyana a taron manema labarai da aka shirya ta kafar intanet a ranar 15 ga wata cewa, baje kolin zai gudana a yanki mai girman gaske, wanda zai kunshi sassan baje koli shida, da suka hada da bangaren abinci da amfanin gona, da bangaren motoci, da bangaren kayayyakin fasaha, da kayayyakin bukatu, da bangaren magunguna da kiwon lafiya, da bangaren hada hadar ayyukan hidima, sai kuma akwai wasu sabbin bangarori hudu a wannan shekara, kamar bangaren kula da lafiyar jama'a da kandagarkin annoba, da tsimin makamashi da kare muhalli, da bangaren tafiye tafiye da kayayyakin wasanni gami da harkokin wasannin motsa jiki.
Gao ya jaddada cewa, a halin da ake ciki na yanayin kandagarki da yaki da annoba, bikin baje kolin karo na uku zai bayar da fifiko matuka kan kiyaye lafiyar al'umma, kuma zai cigaba da yin tsare tsaren da suka dace domin tabbatar da ganin an gudanar da bikin baje kolin cikin nasara a nan gaba.(Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China