Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya taya Sarkin Tonga murnar zagayowar ranar kafuwar kasarsa
2020-11-04 11:00:29        cri

Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika da sako ga Sarki Tupou na shida na kasar Tonga, don taya shi murnar zagayowar ranar kafuwar kasar.

Xi Jinping ya ce a shekarun baya-bayan nan, dangantakar kasashen biyu na samun bunkasuwa cikin sauri, tare da samun ci gaba mai armashi ta fuskar hadin kansu a fannoni daban-daban. Ban da wannan kuma, kasashen biyu na taimakawa juna wajen yakar COVID-19, inda ya ce ta hakan, zumuncin jama'ar kasashen biyu na kara zurfafa. Ya ce Sin na ba bunkasuwar dangantakar kasashen biyu muhimmanci sosai, kuma tana fatan kara hadin kai da Tonga don ingiza dangantakar bangarorin biyu a dukkanin fannoni, bisa manyan tsare-tsare, zuwa wani sabon matsayi, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su ci gajiya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China