Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun gwamnatin Yemen sun fafata da mayakan Houthi a lardin Taiz
2020-11-04 10:07:37        cri
Sojoji masu biyayya ga gwamnatin kasar Yemen sun yi musayar wuta da mayakan 'yan tawayen Houthi a lardin Taiz dake kudu maso yammacin kasar, wani jami'in sojin kasar ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Jami'in sojin wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya ce, wasu yankuna da dama dake lardin na Taiz ta bangaren arewaci sun fuskanci arangama ta tsawon sa'o'i tsakanin dakarun sojojin gwamnati da mayakan Houthi.

Ya ce an kashe mayakan Houthi 15 da sojojin gwamnati 5 kana wasu mutanen da dama sun samu raunuka a sabon fadan da ya barke tsakanin bangarorin biyu.

Majiyar ta kara da cewa, babu wani cigaba da aka samu ta fuskar soji bayan barkewar tashin hankalin wanda ya faru a kusa da gidajen wasu mazauna lardin Taiz.

A ranar Litinin, 'yan tawayen Houthi sun kaddamar da hare-hare da makaman artillery kan yankunan arewaci da gabashi masu makwabtaka da lardin Taiz, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkata fararen hula 7, kamar yadda wasu majiyoyin jami'an lafiyar yankin suka tabbatar.

Dakarun tsaron gwamnatin Yemen, dake samun goyon bayan kawancen sojojin da kasar Saudiyya ke jagoranta, sun jima suna yaki da mayakan 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan dakarun sojojin Iran dake arewaci, gabashi, da kuma yammacin lardin Taiz, rikicin wanda ya soma tun a watan Afrilun shekarar 2015.

Kasar Yemen ya fada yakin basasa ne tun a karshen shekarar 2014, lokacin da mayakan 'yan tawayen Houthi suka kwace yankunan kasar da dama kana suka kwace ikon dukkan lardunan arewacin kasar, wanda ya hada har da babban birnin kasar Sanaa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China