Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar 'yan tawayen Houthi ta Yemen sun lashi takwabin kai hare-hare wurare 300 a cikin Saudiya da hadaddiyar daular Larabawa
2019-05-20 11:27:20        cri
Kamfanin dillancin labarai na Saba, wanda Houthi ke iko da shi ya bada rahoton cewa, kungiyar 'yan tawayen Houthi dake kasar Yemen ta sanar cewa hare haren da aka kaddamar ta jirage marasa matuka a makon jiya kan tankokin man Saudiyya tamkar daura damba ne na hare haren sojojin data shirya kaddamarwa a wurare kusan 300 a kasashen Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa (UAE).

Saba ya bayyana hakan kamar yadda ya jiyo dakarun sojojin Houthi suna bayyana, "Wuraren da kungiyar ke son kai harin sun hada da helkwatar sojoji, da wasu sansanoni, da kuma wasu muhimman kayayyaki a cikin kasashen Saudi Arabia da UAE, da kuma sansanoninsu dake Yemen".

Gidan talabijin na Al Arabiya mallakin kasar Saudiyya ya bayar da labari cewa, a ranar Talata, mayakan 'yan tawayen Houthi sun kaddamar da hare hare ta jirage marasa matuka akan tashoshin man fetur biyu na kasar Saudiyya, lamarin da ya haifar da gobara da 'yar karamar barna.

Kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta suna ta kokarin kai dauki a yakin basasar da ya barke a Yemen tun a shekarar 2015, inda suke yaki da 'yan tawayen Houthi masu alaka da kasar Iran wadanda suka kwace ikon lardunan arewacin kasar Yemen, ciki har da babban birnin kasar Sanaa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China