Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Mutane 40 sun halaka a fadan da ya barke a Aden na kasar Yemen
2019-08-12 10:46:21        cri
Jami'ar kula da harkokin jin kai ta MDD dake kasar Yemen Lise Grande, ta bayyana cewa, kimanin mutane 40 ne suka mutu kana wasu 260 kuma suka jikkata a fadan da ya barke jiya Lahadi tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da na majalisar rikon kwarya dake kudancin kasar (STC).

Da take karin haske cikin wata sanarwa da ta fitar, jami'ar ta ce, fararen hula da dama sun rasa rayukansu baya ga wadanda suka jikkata, tun lokacin da fada ya barke ranar 8 ga watan Agusta a wajen birnin Aden.

Ta ce, abin takaici ne cewa, a lokacin babbar sallah, iyalai na zaman makokin 'yan uwansu da suka mutu, maimakon su yi murnar bikin sallah tare cikin zaman lafiya da jituwa.

Don haka, ta ce, MDD ta damu matuka da rahotannin dake nuna cewa, abinci da ruwa da daf da karewa fararen hula da suka makale a gidajensu

Grande ta bukaci, bangarorin dake gwabza fada da juna, da su kare fararen hula, ta kuma yi kira ga mahukuntan yankin, da su baiwa kungiyoyin agaji damar kaiwa ga mabukata ba tare da gindaya wani sharadi ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China