Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai da harin jami'ar Kabul
2020-11-03 20:15:34        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana matukar takaici, game da harin ta'addanci da ya hallaka a kalla mutane 22, a jami'ar birnin Kabul dake kasar Afghanistan.

Wang Wenbin, wanda ya yi tir da harin na jiya Litinin yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce Sin na matukar adawa da duk wani nau'in aiki na ta'addanci, kuma tana mai mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya hallaka, da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Wang ya kara da cewa, har kullum Sin na matukar adawa da duk wani nau'in hari na ta'addanci, tana kuma goyon bayan gwamnatin Afghanistan da jama'ar kasar, a kokarin su na dakile hare haren ta'addanci, da wanzar da tsaron kasa. Kaza lika a shirye take ta yi aiki da sassan kasa da kasa wajen wanzar da zaman lafiya, da daidaito, da ci gaba, da cimma nasarorin kasar ta Afghanistan nan ba da jimawa ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China