Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan za a tabbatar da zaman lafiya a Afghanistan
2020-03-02 19:01:00        cri
A ranar 29 ga watan Faburairun da ya wuce ne, Amurka ta daddale yarjejeniyar zaman lafiya tare da kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar. A game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian a yau Litinin ya bayyana cewa, Sin na fatan yarjejeniyar za ta kai ga tabbatar da zaman lafiya a kasar Afghanistan, kuma kasar Sin na son ci gaba da ba da tallafi da taimako ga aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan.

Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin da ma wakilan kasashe da kungiyoyin duniya da na shiyya shiyya sun halarci bikin rattaba hannun. Ya ce, Sin na maraba da daddale yarjejeniyar da bangarorin biyu suka yi, wanda a ganinta ke da matukar ma'ana wajen warware matsalolin kasar Afghanistan a siyasance. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China