Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Amurka za ta martaba ka'idojin kasuwa da takara mai tsafta
2020-11-02 19:23:57        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na fatan bangaren Amurka, zai rungumi akidar barin kasuwa ta yi halin ta, da kuma yin takara mai tsafta da sauran sassa.

Wang Wenbin wanda ya bayyana hakan a yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya yi fatan ganin Amurka ta martaba dokokin bunkasa tattalin arziki, da na cinikayya da kasashen duniya suka amincewa, ta kuma samar da yanayin kasuwanci mai nagarta tare da sauran kamfanonin kasa da kasa dake hada hada a Amurkan, cikin adalci da rashin nuna banbanci.

Wang na wadannan kalamai ne a matsayin martani, bayan da alkalin wata kotu dake jihar Pennsylvania na Amurka, ya goyi bayan matakan gwamnatin kasar game da dakatar da manhajar TikTok a Amurka, karkashin umarnin da zai fara aiki tun daga ranar 12 ga watan nan na Nuwamba.

Jami'in na Sin ya kara da cewa, har kullum Sin na adawa da matakin Amurka na nuna fin karfi, ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa, da amfani da karfin mulki wajen muzgunawa kamfanonin kasashen waje. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China