Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Amurka ba ta da ikon kasancewa mai koyarwa saura yadda za su kiyaye hakkin dan Adam
2020-11-02 19:36:52        cri

A kwanan baya ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka, ta fitar da bayani ta shafin yanar gizo, game da batun hakkin dan Adam a kasar Sin, inda ta soki gwamnatin kasar Sin, tana mai cewa wai ba ta martaba hakkin dan Adam, a yayin da take gudanar da harkokin dake shafar yankuna Xinjiang, da Tibet, da kuma Hong Kong, kana ba ta martaba hakkin dan Adam a bangaren 'yancin bin addini a kasar.

Kan wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana yau a nan birnin Beijing cewa, Amurka ba ta da ikon kasancewa mai koyarwa saura yadda za su rika kiyaye hakkin dan Adam, kuma bai dace ba, ta kasance mai kirkirar kwayar cutar siyasa, ko kuma mai yada bayanan karya.

Wang ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da manufar kiyaye hakkin dan Adam, ta mayar da moriyar al'ummun kasar a gaban komai, har ma ta cimma burinta na fitar da al'ummun kasar da yawansu ya kai biliyan 1.4 daga kangin talauci, tare kuma da samun wadata, kuma matsakacin tsawon ran al'ummun kasar ya daga daga 35 zuwa 77, kana ta kafa tsarin ba da ilmi da tsarin tabbatar da zamantakewar al'ummun kasa, da tsarin kiwon lafiya, da tsarin demokuradiya mafiya girma a duniya.

Haka zalika, tana tabbatar da 'yancin nuna ra'ayi, da 'yancin bin addini, da 'yancin gudanar da harkokin kasa na 'yan kananan kabilun kasar bisa doka.

Jami'in ya kara da cewa, Amurka ta kasa kula da hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki, kuma ta kasa kula da matsalar keta hakkin dan Adam ta kasarta, kuma tana shafawa kasar Sin bakin fenti. Ko shakka babu kasar Sin tana adawa da wannan batu, kana tana ganin cewa, ya dace Amurka ta yi la'akari da matsalolin da take fuskanta a bangaren kare hakkin dan Adam, tare kuma da daidaita matsalolin yadda ya kamata. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China