Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kaddamar da shirin hadin gwiwa na SDG a Ghana
2020-11-01 17:09:36        cri

MDD ta kaddamar da shirin tara kudaden aiwatar da ayyukan shirin samar da dawwamammen ci gaba na MDD wato SDGs a kasar Ghana.

Charles Abani, wakilin MDD a kasar Ghana ya ce, samar da kudaden ayyukan shirin hadin gwiwar na SDG, wani muhimmin bangare ne na bunkasa ci gaban al'umma da tattalin arziki da kuma fardadowa wanda MDDr za ta samar da dala miliyan 91 kan kudaden da ake da su domin taimakawa kasar ta Ghana.

A hakika dai, za a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa ayyukan shirin samar da dawwamamen ci gaba na SDG a Ghana, da kuma samar da ingantattun fasahohin kirkire kirkire wadanda za a ba su fifiko wajen ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa wanda zai baiwa kamfanoni masu zaman kansu damammakin zuba jari.

Da yake nuna yabo ga MDD game da bullo da shirin, George Gyan-Baffour, ministan tsare tsaren ci gaban Ghana, ya ce, damar da aka samu ta tsarawa da kuma aiwatar da shirin yadda ya kamata da samar da kudaden gudanar da shirin, za ta taimakawa kasar a kokarinta na cimma nasarar aiwatar da shirin na SDGs a kasar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China