Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Ghana ya yi kira da a sake bude iyakokin Najeriya da aka rufe
2019-11-20 20:09:34        cri

Tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama, ya yi kira da a sake bude iyakokin Najeriya na kasa, domin ci gaba da gudanar da hada hadar tattalin arziki tsakanin kasashen dake shiyyar yammacin Afirka.

Mahama, ya yi wannan kira ne a jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya, yayin wani taro da ya gudana a ranar Talata. Ya ce matakin rufe kan iyakokin Najeriya na kasa, musamman tsakanin kasar da janhuriyar Benin, ya fara haifar da matsi ga kanana da matsakaitan 'yan kasuwar kasashen Ghana, da Cote d'Ivoire, da Togo, wadanda ke dogaro ga kasuwanci tsakanin wadannan kasashe.

Ya ce a matsayin Najeriya na kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, mai kuma masaukin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS, rufe kan iyakokin ta bai dace da manufar kafa ECOWAS ba, wanda daga ciki hadda hada kan kasashe mambobinta, ta yadda za su ci gajiyar juna.

Gwamnatin Najeriya dai ta ba da umarnin rufe kan iyakokin ta na kasa, da wasu kasashe makwaftan ta ne tun cikin watan Agusta, a wani mataki na abun da ta kira dakile ayyukan fasa kwauri, da kawo karshen wasu kalubale na tsaro. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China