Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana za ta yiwa yan kasarta dake ketare rajista gabanin zaben shugaban kasar
2020-07-03 11:00:26        cri

Hukumar zaben kasar Ghana ta ce nan gaba kadan za ta yiwa 'yan kasar da suka cancanci kada kuri'a wadanda suka makale a kasashen waje rajista sakamakon rufe kan iyakokin kasashen sanadiyyar barkewar annobar COVID-19.

Shugabar sashen hulda da jama'a na kasar Sylvia Annor, ta sanar cewa, dokar kasar Ghana ta baiwa hukumar zaben kasar ikon yin rajistar dukkan 'yan kasar Ghanan da suka cancanci kada kuri'a domin su jefa kuri'un su a lokacin babban zaben kasar dake tafe a watan Disamba.

A wata sanarwa, wakilin musamman na babban sakataren MDD na yammacin Afrika da yankin Sahel Mohammed Ibn Chambas, ya karfafawa mutanen kasar Ghana gwiwa da su goyi bayan aikin yin rajistar cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma su dora muhimmanci wajen daukar matakan kandagarkin annobar COVID-19 a lokacin da suka hau layukan yin rajistar babban zaben na bana.

A ranar 7 ga watan Disamba, kasar Ghana za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China